Kimanin shekara daya kenan da kamfanin Facebook da google, suka dauki damarar kawo kashen yada labaran kanzon kurege. Wanda akan yada su a mafi akasarin lokutta masu hadurra.
Shafufukan yanar gizo, an kirkire su ne don su bama mutane damanmaki wajen inganta rayukan su, amma sai ga wasu bata gari na amfani da kafofin wajen karas da wasu labarai da basu da tushe.
Idan akayi la’akari da abun da ya faru a satin da ya wuce, lokacin da aka kai wani hari a babban birnin Las Vegas, wanda ake rade radin cewar wasu mutane dauke da bindiga, su nata harbe-harbe a cikin bainar jama.
Daga bisani wasu sun kirkiri wani shafi don nuna wanda yayi harbin, da bayyanar da wani mutun dauke da bindiga, amma bayanai sun karyata wannan labarin, da aka wallafa a shafin na facebook.
Kwana daya bayan afkuwar abun, sai ga shafin Youtube sun fitar da wani bidiyo, da yake nuna cewar maharban ba mutun daya bane, don haka labarin ya banbanta da yadda wasu ke ayyana shi.
Daga bisani jami’an tsaro sun tabbatar da labarin gaskiya, wanda ya tabbatar da cewar mutun daya ne yayi wannan aika aikan, mai suna Stephen Paddock, wanda har loacin hada wannan labarin, babu masaniyar dalilin shi nayin wannan danyen aikin.
Harin dai da aka kai a ranar 1 ga watan Oktoba, yayi sanadiyar mutuwar mutane 58 da raunata mutane da dama. Don haka kamfanonin biyu suna aiki tukutu don kawo karshen wannan danyen aikin.