Facebook Zasu Kaddamar Da Sabon Tsarin 'Fuska Bada Sarari'

Kamfanin Facebook, sun kaddamar da nasu sabon tsarin nuna fuska ka samu sarari, wannan wani tsari ne da kamfanin Apple suka fara fitar da shi, don magance matsalar satar fasali.

Gamasu amfani da sabuwar wayar iPhone 8 ko iPhone 8+, sukanyi amfani da fuskokin su wajen bude wayar, a duk lokacin da mutun ya bukaci bude wayar shi, zai kawai kalli wayar sai ta saita tsarin furkar shi kana ta bude.

Wannan wata damace da koda an sace wayar mutun, baza’a iya bude ta ba, sai mai asalin wayar kawai zai iya amfani da ita, wannan wani sabon tsari ne da kimiyyar zamani ta kawo, an wuce yayin amfani da zanen hannu wajen bude waya.

Tsarin zai taimaka matuka ga mutane da suka manta da wayar su, ko suka tsinci kansu a yanayin tafiya, a lokutta da dama, idan mutun ya manta da lambar sirrin bude asusun shi, akan tambayi mutun lambar waya ko email nashi don a aika mishi da sabuwar lamba.

Amma wannan sabon tsarin, zai ba mutun damar koda baya tare da wayar shi, ko asusun email nashi zai iya bude shafin shi na facebook, a kowane hali ya tsinci kan shi, musamman idan zai iya kallon kyamarar waya ko kwamfutar da yake da bukatar bude shafin na shi.

Wannan sabon tsarin zai taimaka matuka wajen magance satar bayanai, wanda fuskar mutun dayace zata yi dai-dai da asusun shi. Sabon tsarin dai na fuskantar suka daga wajen mutane da dama, amma kamfanin suna kokarin su wajen ganin sun inganta tsarin.