Wani mawaki kuma mai fasara a fina finai Sadiq Salihu, ya ce yana da burin inganta harshen Hausa domin saukin fahimtar harshen ga jama’a.
A halin yanzu harshe yayi nisa wajan bunkasa a sasssan duniya in ji mai fassara Sadiq Salihu Abubakar wanda aka fi sani da ‘ Buzu dan Fullo mai suburbuda’
Ya bayyana haka ne a yayin hira da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, a birnin Kano, inda yake cewa ya tsundumaa ga harkar fassara ne ganin cewar a wani bincike da aka gudanar a kan harshe ya nuna cewar harshen Hausa na daya daga cikin harsuna biyar da suka fi kowanne harshe nisan zango da habbaka a duniya.
Mai suburbuda ya ce harshen na da wahalar fassara mussamam ma wasu kalmomi da babu su a harshen Hausa, wanda dole ta sanya suka fito da wasu kalmomi da al’umma tuni suka karbi sabbin kalmomin.
Yan a mai cewa yanzu haka yana fasara fina finan barkwanci da ake kira “Cartoon” a turance wanda kuma jama’a suka yi na’am dashi.
Ya ce kalubalen da sukan fuskanta dai bai wuce yar tirjiya da suka samu daga alumma wanda al’adace ta dan Adam na kin amincewa da sabon abu da zarar ya shigo gari.
Facebook Forum