Kamfanin YouTube ya bada sanarwar kaddamar da sabuwar manhajar YouTube Go, a taron babban kamfanin na’ura mai kwakwalwa Google, da aka gudanar kwanan nan.
Kamfanin YouTube, ya yi wannan kokari ne domin saukakawa masu amfani da kafar da ke fuskantar kalubalen yawan amfani da Data da kuma rashin karfin network a kasashe masu tasowa irin su Najeriya .
Kamfanin zai ci gaba da inganta manhajar ta hanyar amfani da ra’ayoyin jama’a bayan sun fara amfani da manhajar.
Da yake jawabi, Johanna Wright, mai gudanar da samfurin VP a kamfanin YouTube, ya ce an tsara wannan manhaja ne domin la’akari da kalubalen da masu amfani da YouTube ke fuskanta a kasashe irin su Najeriya.
Manhajar YouTube Go, zata saukakawa jama’a su kalli hotuna ko bidiyon da suke bukata cikin sauki ba tare da amfani da Data mai yawa ba.
Sabuwar manhajar nada nau’uka daban daban kama daga na sauya hasken hoton bidiyo da kaloli da kuma sauransu.
Facebook Forum