Na'urar 'Drone' Kirar Kamfanin Facebook, Zata Samar Da Yanar Gizo Kyauta A Duniya.

A karo na biyu, kamfanin Facebook sun kaddamar, da samun nasarar aika jirgi mai tashi da kanshi ‘Drone’ cikin sararrin samaniya. Na’urar dai tayi shawagi a cikin sararrin samaniya. Wanda babban burin shugaban kamfanin na Facebook shine. A kai lokacin da wannan jirgin zai samarma kimanin mutane sama da billiyan hudu yanar gizo a fadin duniya.

A cewar shugaban kamfanin Mark, har a wannan karnin akwai milliyoyin mutane a fadin duniya da suke rayuwa cikin duhun yanar gizo. Basu da masaniyar me duniya take ciki, hakan kuwa na faruwa ne a sanadiyar rashin yanar gizo.

Amma wannan tsarin zai bama mutane damar sanin me ke faruwa a duniya, ba tare da sun kashe kudin su wajen siyan intanet ba.

Ya kara da cewar, idan har na’uarar da suka lakama suna ‘Aquila’ ta gama kammaluwa, zasu aikata cikin duniyar wata. Na’urar dai nada nauyin buhun siminti 9, kuma tana dauke da wasu nau’rori da suke taimakamata gabatar da aiki cikin sauki.

Shugaban dai ya kara da cewar, babu wani kamfani da ya taba kera jirgi da ke yawo cikin sararrin samaniya, batare da mutun yana juya akalar jirgin ba, amma suna yunkurin yin haka, a wannan karni na 21.