Rashin Isasshen Bacci, Na Haifar Da Karin Cututtuka A Jikin Dan'adam

Lack of Sleep

Karancin bacci ga dan’adam, na haddasa cututtuka masu yawa a jikin mutun. Mutane masu dauke da cutar zuciya, da ciwon suga, na tare da hadarin zafafa cutar su, da kashi 2, idan har jikin su baya samun isashen bacci.

Wannan bayanan suna kunshe ne a cikin wani sabon bincike da aka wallafar. Masana sun kara da cewar, a yayin da jikin mutun baya samun wadataccen bacci, wanda hakan yake shafar jijiyoyin jinni, da suke watsa jinni a jikin mutun, da ba wasu gabobi damar samun walwala.

Mafi akasarin mutane dake dauke da ciwon hawan jinni, jikin su na bukatar baccin da bai kasa da awowi 6, a duk dare. Binciken da aka gudanar akan mutane 1,344 wanda sakamakon ya nuna cewar kashi 40 na mutanen.

Basu samun bacci, wanda hakan yake shafar lafiyar su, da kokarin kara hauhawan ko kamuwa da wasu sababbin cututtuka. Hakan kuma yayi nuni da cewar, mutane da basu samun isasshen bacci a kullun.

Su gaggauta ganin likita, don samun taimako da zai nisanta su da kamuwa, da cututtuka da suka hada da hawan jinni, da makamantansu. Rashin bacci mai yawa bai tsaya kawai ga lafiyar jiki ba, har yakan shafi kwakwalwar dan'adam.