Akwai bukatar masu hannu da shuni da gwamnatoci su shigo cikin harkar wakokin mawakan Hausa, don inganta masana'antar wajen samar da kudaden shiga inji mai wakar hip-hop Musa Ragaa.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir a garin Kanon Dabo.
Musa Ragaa ya ce babban abinda da ke ci wa matasan mawaka tuwo a kwarya bai wuce yadda ake yi wa harkar rikon sakainar kashi ba, ba'a baiwa harkar muhimmanci.
Ragaa ya ce a mafi yawan lokutan ana kallon mawaka a matsayin marasa tarbiya da da'a maimakon wasu mutane da ke inganata harshen Hausa tare da fadakarwa da nishadatarwa a lokaci daya
Ya ce baban burin sa ya bar baya ko da baya duk wanda ya ji wakar sa zai amfana ya kuma cewar Ragaa ya bar wa'azi a wakokinsa.