An bayan karbar bashin kayayyaki da abokan huldan kasuwanci suke yi a matsayin daya daga ciki abubuwan dake jawon koma baya ga kananan ‘yan kasuwa.
Malama Halima Labaran, wata karamar ‘yan kasuwa tace karbar bashin da jama’a ke yawan yi ya haddasa mata karayar jarin na wajen bunkasa saye da sayarwar da take yi.
Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA yau a birnin Kano dake Najeriya.
Malama Halima, ta ce a da jarin ta ya bunkasa amma a yanzu an samu koma baya ta fuskar jarin tafiyar da kasuwanci yadda ya kamata.
Ta kara da cewa ta shafe kimanin shekaru goma sha biyar (15), tana wannan sana’a domin ta zamo mai dogaro da kai, kuma da wannan sana’a ne ma har ta kai ta da gina gida bayan kashe kananun bukuta na yau da kullum
Ta kuma ja hankalin matasa da su jajirice wajen neman nasu na kansu domin kuwa yau yadda rayuwa ta canza duk wanda ya kwanta lallai yana tare da bacin rai da nadama.