Kamfanin Apple Zasu Kaddamar Da Sababbin Cigaba A MacBook Air

A nasa tsammanin kamfanin Apple, zasu bayyanar da sababbin cigaba da suke yunkurin sakawa a sababbin kwamfutocin su, a lokacin wani taron cigaba, na shekara-shekara da suke gudanarwa, cikin watan Yuli idan Allah ya kai rai.

A rahoton da kamfanin dillancin labarai na ‘Bloomberg’ suka wallafa, cewar kamfanin na Apple na kara wannan azamar ne, don tserema sa’o’I, ganin yadda abokan hamayyar su na kamfanin Microsoft ke kokarin shiga gaban su a kimiyyar fasaha.

A cewar rahoton, kamfanin na Apple zasu kaddamar da sababbin kwamfutar laptop guda uku, Wanda ita ‘Macbook Pro’ da aka kayatar da karfin gudu ta cikin gaggawa, kana da ‘Macbook Air’ zasu zo da girman inci 12 da inci 13. Suna kuma dauke da sabon tsarin ‘Intel’ zubi na 7.

Kwamfutar laptop ta kamfanin Apple ita ke kawoma kamfanin kashi 11%, na kudin shiga a shekara, kimanin dallar Amurka billiyan $216. Inda wayar iPhone kan kawo kashi 2% cikin 3% na baki daya kudin shiga na kamfanin.

Sun kara da cewar sababbin kwamfutocin, za suzo da kama irin tsohuwar kwamfutar, inda kawai zasu sha banbban shine a tsarin ciki 'software'. Shekaru 7 kenan da kamfanin suka kaddamar da kwamfutar ‘Macbook, haka fiye da shekara daya kenan da suka fito da Macbook Air.