Lokaci yayi da mata matasa zasu canza tunaninsu, musamman na al’amuran da suka shafi zaman aure da soyayya, domin samun al’umma mai inganci, a cewar shahararriyar mawakiyar Hausa da Faransanci Sa’ida Adam.
Matashiyar mawakiyar dai ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da DandalinVOA a yau. Saida Adam, matashiyar mawaki wacce ta fi raja’a a wakokin rayuwa da al’amuran da suka shafi harkokin mata.
Ta ce tana duba matsalolin rashin kamun kai, da rashin zaman gidan aure da yawan buri da mata matasa ke yi a yanzu. Sai ta kara da cewar, wakokinta sun fi gabatar da nasihohi ga mata, tare da jan hankali al'umma, dama iyaye su sani cewar hakkokin sun rataya a wuyansu na tarbiyartar da diya mata.
Mawakiya Sa’ida, dai na yin wakokinta ne da harshen Hausa da kuma Faransanci kasancewar an haife ta a kasar Nijar, ta kuma yi rayuwarta a kasar Cote D’Ivoire, inda ta kamala karantunta a can.
Ta kara da cewar, ta gamsu da sakonnin da take isarwa ga ‘yan uwa matasa, kuma tana da burin samun fice kamar ragowar mawaka, inda take cewa takan fito a wasu fina-finan Kannywood duk a yunkurin ilmantar da masu sauraro da kallo.