Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fina-Finan Hausa Na Wannan Karnin, Basa Nuna Al'adun Malan Bahaushe!


Tambaya Matar Malan Mamman
Tambaya Matar Malan Mamman

Shirin nishadi na DandalinVOA ya karbi bakoncin, jaruma, da ta ga jiya ta ga yau a harkar fina-finan Hausa . Hauwa Haruna, wace aka fi sani da ‘Ladin Cima’ ko ‘Tambaya Matar Malan Mamman’ wacce ta ce ta fara fitowa fim tun ana biyan ta naira goma, bayan tayi fina-finai kyauta irinsu shahararren fim din Shehu Umar.

Ta kara da cewa, tun ana zuwa garin Kaduna domin yin fim, wanda a wancan lokacin babu gidan talabijin a jihar Kano. A wancan lokaci har sai an tafi kaduna, kuma suna harkar fim a kyauta, da wasu fitattu kamar irin su Doron Maje da Alkali kuliya.

Tambaya, ta ce sai bayan da aka bude gidan talabijin na NTA Kano, a wannan lokaci ne aka fara basu kudi naira goma, ta kara da cewa harkar fim a da, da yanzu akwai bambanci, domin kuwa ana nuna tsantsar dabi’un malan Bahaushe ne, na kunya da al’adu da suka kamata, inda bai yuwa a nuno mata da miji a cikin daki daya, amma a yanzu fa?

Amma yanzu zamani ya zo, da har ana nuno su tare a kan gado, baya ga shigo da wasu yaruka daban da aka hada a fina-finan malan Bahaushe, wanda hakan ya tabbatar da cewar, ba al’ada ake nunawa ba, don kuwa mafi akasari al’adun kasashen waje ake nunawa, na zamani masu kyau da marasa kyau.

Tambaya matar Malan Mamman, ta ce bata fuskantar wani kalubale, a harkar fina-finai a iya zamanta, domin kuwa ana bata duk girma da ya kamata na matsayinta uwa a cikin masana’antar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG