Tekun Waka: Sana'ar Waka Tayimun Komai a Rayuwa!

Tekun Waka

Kabiru Uba Ahmad wanda aka fi sani da ‘Tekun Waka’ mawakin Hausa wanda ya fi raja’a a wakokin aure da soyayya, inda ya maida hankali ga wakokin biki, ko ba komai yana samun kudi ta hakan.

Tekun waka ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da wakiliyar DandalinVOA a yau.

Kamar ko wane mawaki, yace yana isar da sakoninsa ta wakar aure, inda yake fadakar da ma’aurata muhimmancin zamantakewa, da halayyar da ake tsinta a zaman aure.

Yace yakan taba wakar siyasa, domin ita sai an biya kudi kuma shi ya mai da waka a matsayin, ko da yake tekon waka yace ya shafe shekaru fiye da 10 yana yinta .

Ya kara da cewa ya samu babban alfanu ta sanadiyar waka, domin tayi masa komai, ya gina studio na sana'a a kansa, inda yake rera wakokinsa har illa yau babban burinsa bai wuce jama’a su amfana da abinda yake isar wa ba.