Malama Salamatu Ibrahim, mai rajin kare hakkin ‘yaya mata, tace ga dukkanin addinan duniya, babu wani addini da ya baiwa diya mace dama wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata baya ga nuna daraja ga mata kamar addinin Isilama.
Tsohuwar shugabar kungiyar 'yan uwa mata musulmi ta Nijeriya, Malama Salamatu Ibrahim, ta bayyana haka a yayin zantawa da wakiliyar DandalinVOA a yau a garin Kano.
Malama Salamatu, ta ce Musulunci ya daukaka mace inda a cikin Al-Qurani mai girma, Allah yace mace rabin jikin na namiji ce, kuma tana da hakkin na a llura da ita, a kiyaye mata addininta, da kiyaye mata jinsinta, da ita da dukiyarta. Wasu daga cikin hakkokin mace, domin dai-dai take da ‘Da namiji wajen mutuntawa da sauransu.
Ta kara da cewa, a yanzu lalura ce zata sanya mace fita tayi aikin asibit, ko na koyarwa, da ma siyasa domin ta wakilci 'yan uwanta mata, musulunci ya bukaci mace ta fito inda ake bukatarta.
Ya zama wajibi mace ta fito ta taimakawa 'yar uwarta mace maimakon ta bari wani namiji yana maye gurbin, da ya kamata ace mace ke wannan aikin, kamar aikin asibiti.
Akwai bukatar mata da yawa su fito don taimakawa wajen cigaban 'yan uwa mata da al'umma, da duk wata gudunmawa da ya kamata su bada a matsayin su na mata, don cigaban kasa.