Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata A Ba Mata Dama Su Taka Rawa A Harkokin Siyasa-Inji Aisha Yakubu Mai Jama’a


Aisha Yakubu Mai Jama’a
Aisha Yakubu Mai Jama’a

Allah ya albarkace ni da haihuwar ‘ya’ya dai dai har guda takwas kana Allah ya nufe ni da shiga makarantar gaba da sakandare domin karo karatu a cewar wata fitatticiyar ‘yar siyasa Aisha Yakubu Mai Jama’a.

Malamar ta bayyana cewa ta koma makaranta a shekarar ta 2009, inda ta karanci Public administration kuma a hallin yanzu take karatun HND wato kwatankwacin karatun digiri.

Ta ce a matsayinta na ‘yar siyasa, ta fahimci cewa a halin yanzu ba’a baiwa mata damar damawa da su a harkar siyasa inda ta ce mafi yawa maza basa son mata su shiga cikin siyasa sun mai da harkar kamar gado ko sana’a.

Aisha Mai Jama’a, ta ce zai yi wuya mace ta fito neman takara ba tare da delegate ko agent sun kawo mata cikas ba, daga karshe ta bayyana cewa abin kunya ne mace ta fito sa’annan ta gaza yiwa al’ummar ta hakan ne ya sa da zarar ta samu nasara babban muradinta a rayuwa shine ta cika alkwarin da ta daukar wa al'ummar ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:56 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG