Arsen Wenger: Ya Daura Laifin Rashin Nasara Ga Laurent Koscielny!

Shugaban Klob Din Arsenal Arsen Wenger.

Shugaban kungiyar kwallon kafar Arsenal, Arsene Wenger, ya daura laifin rashin nasarar da sukayi, akan mataimakin kaftin na klob din su Laurent Koscielny, biyo bayan wasan da aka gwabza jiya Laraba. Inda aka tashi da ci 5-1, tsakanin klob din Arsenal da Bayen Munich. Kungiyar dai ta koma mataki na 10-2 a wasan zakaru.

Bayan an ci su 5-1 sai dan wasa Theo Walcott ya saka musu kwallo a raga, jim kadan kamin korar mataimakin kaftin Laurent, cikin mintoci 54 da fara wasa. Wannan wani babban kalubale ne ga dan wasa Robert na klob din Bayern.

Shi dai dan wasa Robert shi yaci duk kwallaye da aka saka a raga na fenaliti da aka buga, kana ‘yan wasan Bayern sun nuna rashin jin dadin su ga ‘yan wasa 10 na klon din Arsenal, biyo bayan fitar da dan wasa Laurent da akayi. Kuma bazai buga sauran wasa na gaba ba.

A cewar manajan klob din Arsenal Arsen Wenger, “Mun samar da wasan da muke so, amma dai bamu da sa’a” ya fadi haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a filin wasa na Emirates.

Duk dai da cewar wasu matakan da alkalin wasan ya dauka, suna da wuyar fahimta. Domin kuwa satar gida da dan wasa Robert, yayi bai kamata a bada fenaliti ba. Bugu da kari har ma da bada jan kati, gaskiya hakan ya kashe muna gwiwa, kana kuma yasa bamu samu karfin iya kammala wasan cikin jin dadi ba.