Dan wasan da yafi kowane dan kwallo tsada a duniya wanda yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dake Ingila, Paul Pogba ya zama dan wasa na farko a kakar wasan Firimiya lig na kasar Ingila a bana, da ya samu nasarar rarraba kwallo (passing) sama da 1000 yayin da yake taka leda wa kungiyarsa .
Wani bincike da masu bibiyar kwallon kafar Ingila, sukayi ya nuna cewa, Pogba ya rarraba kwalo har sau 1029, yayin karawa da abokan hamayya.
Bayan haka a matakin kwarewar Paul Pogba wajan raba kwallaye yayin wasa ya kai matakin kashi 83.05 cikin dari. Manchester United, ta sayo dan wasan daga Kungiyar Juventus na kasar Itali akan kudi fam miliyan £89.
Jordan Henderson, na kungiyar Liverpool, ke rufa masa baya a matsayi na biyu da samun nasarar rarraba kwallo har sau 987 yayin da yake wasa a kungiyarsa.
Sai Mesut Ozil, na Arsenal ke a matsayi na uku da raba kwallaye tsakanin ‘yan wasa yayin karawa da abokan hamayya sau 954.
Kungiyar ta Manchester united, tana mataki na shida a teburin firimiya lig na kasar Ingila