Ina rera waka da tsintsar Hausa domin ingantawa tare da dawo da martabar harshen mussamam ma a tsakanin matasa inji Mohammad Sani, wanda aka fi sani da Saniyo M Inuwa.
Saniyo M Inuwa, matashin mawaki ya kara da cewa a yanzu matasa basu da ingantacciyar Hausa, cewarsa yanzu sai ka ga mutum gaba da baya Bahaushe ne amma bashi da daidaitaciyar Hausa, hakanne ya sa yake yawan sanya Karin Magana a wakokinsa.
Ya kara da cewa abin takaici ne yadda harshen Hausa, ke neman gushewa kuma ya zamo wajibi ya bada tasa gudunmuwar don inganta ta.
Saniyo ya ce hakika Hausa ita ce tushen malam Bahaushe, amma sannu a hankali harshen na gushewa, kuma waka ita ce hanya mafi sauki wajen ingantawa tare da raya harshen.
Your browser doesn’t support HTML5