Babban kalubalen da na ke fuskanta bai wuce yadda wasu daga cikin masoyana ke kira akai-akai bila adadin a lokaci guda, batare da li’akari da yanayin da mutun ke ciki ba inji mawaki Umar Sayyidi Gadon-kaya.
Matashin mawakin da ya samu lambar yabo ta girma wadda ake ba shahararrrun mawaka masu tashe a jihar Bauchi, a shekarar da ta gabata ya ce yawan kiran da wasu daga cikin masoyansu ke yi yana ci musu tuwo a kwarya domin basa li’akari da cewar ba a kowanne lokaci ne suke samun damar daga wayoyinsu ba.
Ya kuma kara da cewa tun yana dan karamin yaro yake da burin rera waka domin isar da sakonnin fadakarwa tare da nishadantar a lokaci guda.
Daga karshe yayi Karin bayanin cewa a halin da ake ciki, yanzu burinsa ya cika domin kuwa, a mafi yawancin lokuta ya kan samu wayoyin wasu daga cikin masoyansa da kan kira domin bayyana masa irin yadda sakonninda yake isarwa ta hanyar waka na sa wasu da dama canza halayensu.