Taimakawa mata akan aiyukan gida da wasu mazaje keyi yanada alfanu domin yana kara dankon soyayya tsakanin ma’aurata da kuma kara girmamawa daga mata zuwa ga mijinta.
Malama Lami Sumayya ce ta furta haka a filin dandalinvoa na samartaka, tana mai cewa samun yi walwala da iyalai a gida yana dinke duk wata baraka idan ta kunno kai.
Tace duk mazajen dake taimakawa matansu da aikin gida tabaci hakika sun san abinda ya dace kuma ace hannu daya baya daukar jinka.
Malama, Sumayya, ta kuma ja hankalin mazaje masu taimakawa iyalansu dasu guji jin surutan mutanen da basu da tausayin taimakawa nasu iyalin, tana mai cewa duk wanda yake taimakawa iyalinsa yana karawa kansa kwanciyar hankalin ne.
Ta kuma yi Allah wadai masu girma kai masu ganin cewa ya ya zasu nemo abinci kuma su taimakamata a aikin gida ta kara da cewa wannan duk rashin fahimta ne.