Na Kware Wajan Dabarun Yi Wa Hotunan Bidyo Kwaskwarima: Abba Edita

Abba Edita

Na samu kuzarin fara sana’ar edita, ko hada fina-finai ne a sakamakon wata rana ina kallon wani fim sai na lura muryar fim din bata fita, kuma ina matukar son cigaba da kallonsa inji Abba Ya'u Abdulkarim.

Daga wannan lokaci ne ya fara gwada daukar hoto da wayoyar hannu, daga bisani kuma ya je ya sami wani wanda ya iya harkar hada fim, ko edita har ya gwada dora murya kan hoto, sai wani abokinsa ya hada shi da Yusuf Magarya, inda daga nan ne ya tsunduma harkar fim gadan-gadan.

Matashin ya kara da cewa ya fi mayar da hankali wajen yi wa hotunan bidiyo kwaskwarima da kara musu armashi domin su kayatar da masu kallo kuma a cewarsa da haka ne ya samawa kansa sana’ar dogaro da kai har ta kai shi ga yin aiki da wasu fitattatun daraktoci.

Abba edita, ya kara da cewa burinsa ya inganta iliminsa na harkar editin mussamam ma ta fannin special effect, wato yin dabarun hada bidiyo domin ya fito kamar da gaske.

Your browser doesn’t support HTML5

Na Kware Wajan Dabarun Yi Wa Hotunan Bidyo Kwaskwarima: Abba Edita