Hukumar dake kula da sha'anin kwallon kafa ta nahiyar kasashen Afirka CAF tace tana shirye shiye domin inganta filayen wasannin kwallon kafa musamman a wasannin da za'a yi na cin kofin kasashen Afirka na shekara 2019, a kasar kamaru.
hukumar tace daukan matakin gyaran ya biyo bayan korafe korafe da suka samu ne daga wasu masu horas da ‘yan wasan kwallon kafa na kasashen Afirka da suka buga a gasar da akayi ta Bana a kasar Gabon, inda wasu masu horaswa suka ce sanadiyar rashin inganceccen filin wasa ne ya hana ‘yan wasansu tabuka wani abun kirki ya kuma jawo samun raunuka ga ‘yan kwallo, don haka CAF tace wannan ya zamo dole ta duba dan a gyara a gaba
A tarayyan Najeriya kuwa bangaren firimiya lig na shekarar 2016/2017 mako na 7 a jiya an buga wasu wasanni Kamar haka Abia Warriors tayi kunnen doki 1-1 da Sunshine
Remo Starts 0-1 Niger Tornadoes
Gombe United ta samu nasara akan Nasarawa United daci 1-0
Plateau United ta doke El-kanemi warrior da kwallaye 2-0
A yau kuma za'a buga wasu daga cikin wasan Tsakanin Enyimba da Akwa United
ABS FC zata karbi bakuncin MFM F
Har yanzu Plateau United ke jan ragamar teburin da maki 17.