Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Haramtawa Karin Wasu Mutane Hudu Gudanar Da Harkokin Kwallon Kafa A Najeriya


Newly elected FIFA president Gianni Infantino of Switzerland during a press conference after the second election round during the extraordinary FIFA congress in Zurich, Switzerland, Feb. 26, 2016.
Newly elected FIFA president Gianni Infantino of Switzerland during a press conference after the second election round during the extraordinary FIFA congress in Zurich, Switzerland, Feb. 26, 2016.

A jiya Talata ne Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta kakabawa wasu karin mutane hudu takunkumi da suke da hannu cikin ringingimun shugabanci a hukumar kwallon kafa ta Najeriya, akan gudanar da harkokin kwallon kafa.

FIFA tace kwamitinta na ladabtarwa ya yanke shawarar haramtawa Chris Giwa da wasu mutane hudu shiga duk wasu harkokin kwallon kafa har tsawon shekaru biyar.

Sauran mutane sun hada da Muazu Suleyman, Yahaya Adama, Sani Fema da kuma Johnson Effiong. A wani sanarwa da FIFA ta dora a shafinta na yanar gizo, tace wannan takunkumin zai shafi duk harkokin wasa a fadin duniya baki daya.

Giwa, tsohon mai kungiyar wasa ta Giwa FC a birnin Jos, dake jihar Filato, ya nace tun cikin watan Agustan shekarar 2014 cewar shine ya lashe zabe don haka shine shugaban humukar NFF bisa doka. An musunta sakamakon zaben wanda hakan ne ya janyo hankalin hukumar FIFA a kan wannan lamari har ya kai ga FIFA ta yi barazanan dakatar da Nigeria cikin harkokinta har sai an sake gudanar da zabe.

A zaben na biyu Amaju Pinnick ya lashe zabe kuma ya zama shugaban hukumar NFF amma tun wannan lokaci ne Giwa ya kai hukumar kotu yana kalubalantartar shugabancin Pinnick. A cikin watan Mayun bara NFF ta haramtawa Giwa da magoya bayansa daukar kansu a matsayin jami’an hukumar saboda kai harkokin kwallo kotu ya sabawa dokokin FIFA.

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ita kuma ta tabbatar da wannan takunkumin na FIFA.

XS
SM
MD
LG