Jajircewa Cikin Aiki Na Kaiwa Ga Nasarori; Jamila Ibrahim

Malama Jamila Ibrahim

Kwazona da jajircewa a wajen aikina ya sa na samu Karin girma har sau uku a shekara guda, in ji Jamila Ibrahim, kuma ta bayyanawa wakiliyar DandanlinVOA Baraka Bashir a wata hira da suka yi da ita a Kano .

Jamila Ibrahim, dai ma’aikaciyar makarantar firamare ce wacce ta fusanci kalubale da dama kafin ta cimma burinta, ta ce a lokacin da take koyarwa ta fuskanci matsaloli daga wajen abokan aki inda wasu ke tunanin cewa ta nuna jajircewa ne kafin aka bata shugabanci makaranta.

Amma duk da cecekucen da abokan aikinta ke nuna mata hakan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba har sai da ta kai matsayin da take wato (early child center classes) daga nan sai wata dama daga Esspin- DFID kungiyar kasashen waje da ke aiki akan ilimi.

Duk da cewa akwai kalubale da yawancin mata daga arewacin Najeriya kan fusnkata a yayinda suke neman ilimi, kama daga al’umma, iyali da sauransu, hakan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba, ta dalilin haka ne ta ke kira ga sauran mata musamman matasa domin tashi tsaye wajan nemen ilimi domin akwai alfanu.

Your browser doesn’t support HTML5

Jajircewa Cikin Aiki Na Kaiwa Ga Nasarori; Jamila Ibrahim