Kungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya Da Fasa Ta Janye Yajin Aiki
WASHINGTON D.C —
A Najeriya, kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasa ta kawo ga karshen yajin aiki na kwanaki bakwai data umurci malaman kwaleji a duk fadin kasar.
Wannan tsayar da yajin aikin bawai tana nufin an janye yajin aikin kwata kwata bane. Shugaban kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha comrade Usman Yusufu dutsi, a tattunawarsa da wakilinmu abdulwahab muhammad ya shaida masa cewa ana cigaba da tattunawa da hukumomin kasa.
Comrade Muhammed Bala Yakubu, shugaban kungiyarcv malamai na kwalejin kimiyya da fasaha dake jihar Bauchi ya yi Karin bayanin cewa sun koma aiki da misalign karfe goma shabiyu na rana bisa umurnin uwar kungiyar malamai ta kasa.
Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.