A duk farkon shekara a garin Sanliurfa, yankin kudu maso gabashin kasar Turkiya, akan gabatar da wata gasa, ta Tantabaru da sukafi kyau. Masa a yankin kanyi kiwon tantabaru, kuma sukan kawatar da su, wajen saka musu dan-kunne, sarka, zobe, da abun hannu.
A lokacin bukin akan duba aga wace tantabara tafi kyawon gashi, kala, kana da irin abubuwan kyale-kyale da aka saka mata. Mutane kan kashe kudade masu yawa, wajen siyan tantabara da take da gashi ko kala mai kyau.
Kudin tantabara daya kan iya kaiwa dallar Amurka $80 dai-dai da naira dubu ashirin da biyar. Duk kuwa tantabarar da ta lashe gasar, mai tantabarar zai samu kudi masu yawa. A cewar wani matashi Ismail Ozbek, yana kiwon tantabaru sama da dari biyu, kuma yakan siyar da su ga masu bukata.
Gasar da suke gabatarwa na tantabarar da tafi kyau, gasace da take da tsohon tarihi a yankin. Kuma suna son gasar matuka, don tana kawo zumunta a tsakanin matasa, domin kuwa kowa yakan zoda ta tashi nau’in basira wajen kawatar da tantabarar shi.