Idan har bayanan da masana taurari suka yi ya zamo gaskiya, to yadda muke kallon taurari cikin dare zai canja sosai nan da 'yan shekaru kadan.
Masana taurari sun ce zai yiwu bil Adama ya kalli hadewar wasu tagwayen taurari biyu, abinda zai sanya su yi bindiga cikin shekarar 2022, watau nan da shekara biyar ke nan, abinda zai haifar da wani irin tauraro mai haske, amma mai launin ja da ake kira "Red Nova" a turance.
Wadannan tagwayen taurari suna bangaren sararin samaniya da ake kira Cygnus Constellation, wanda nisansa daga duniyar bil Adama ya kai tafiyar walkiya na shekaru 1,800. Ma'ana, abinda masana taurarin suke fada ya riga ma da ya faru tun shekaru 1,800 da suka shige, amma hasken abkuwar ne bai iso nan ba tukuna.
A saboda haka, hasashe suke yi a yau na abinda bil Adama zai iya gani a shekarar 2022, bisa la'akari da abubuwan da suka lura da su game da wadannan tagwayen taurari da kuma nisansu daga doron kasar da bil Adama yake kai.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Farfesa Lawrence Molnar na Jami'ar Calvin College dake garin Grand Rapids a Jihar Michigan, da dalibansa da kuma wasu masana taurari 'yan'uwansa a dalkin hangen samaniya na Apache Point Observatory a Jihar New Mexico da Jami'ar Wyoming.
Sun bayyana wannan hasashe nasu a wajen taro na 229 na Kungiyar Masana Taurari ta Amurka a Grapevine dake Jihar Texas.
An jima ana nazarin wadannan tagwayen taurari, amma a shekarar 2013, masana taurari sun lura da sauyin haskensu. Da suka kara bincike sosai, Molnar da sauran masanan dake tare da shi sun gano cewa taurarin biyu suna kara kusantar juna.
Masana taurarin sun auna bayanan da suka gano da abinda ya faru lokacin hadewar wasu tagwayen taurari da ake kira V1309 Scorpii har suka zamo Red Nova, sai suka gano cewa wadannan tagwayen taurarin ma ana dab da ganin hadewarsu ne.
Idan har wadannan tagwayen taurarin dake can nesa sosai suka hade suka yi bindigar da zata haddasa jan tauraro mai haske, za a iya ganinsa ba tare da yin amfani da gbilashin hango nesa ba a bangaren sararin samaniya da ake kira Cygnus, wanda ke arewa.