Fim din Umar Sanda ya fuskanci kalubale da dama daga al’umma akan cewar ya saci fim din ne daga fim din India, ba tare da la’akari da cewar hakan ya hallarta ba Inji Mai Bada Umarni Kamal Alkali.
Jigon labari akan wata yarinya da za’a yi wa fyade Allah ya bata sa’a har akayi rashin sa’a mai fyaden ya fadi ya mutu, na nuni ne da yadda mace zata kare kanta idan ta sami kanta a yanayin fyade makamacin wanna.
Kamal Alkali, ya ce ya dauki wani fim ne na India sakamakon labarin fim din ya zo daidai da irin labarin da yake son fitarwa a wannan lokaci wanda ya danganci fyade, ko da yake ya bayyana cewa zamani ya zo da babu laifin idan ka dauki labari daga wani fim ka wallafi shi a naka harshen matuka zaka bayyana a farko fim din cewa ga daga inda ka samo labarin.
Mai bada umurnin ya kara da cewa kamar yadda shugabanni ke ta kokarin cewar mutane su rungumi dabi’unmu na gari, bai ga laifi a fito da harkar fyade a fim ba kasancewa a yanzu haka dabi’ar da ke ciwa mutane tuwo a kwarya Kenan, kuma ko da ake cewa ya sata daga wani fim ai suma Indiyawa daga wani littafi na kasar China suka dauka.
Daga karshe ya kalubalanci mutane da cewar da ba’a fassara wannan fim na India a harshen Hausa ba, lailai da bazasu fahimci cewar ya kwaikwayi fim din India ba.
Ya kara da cewa abin sha’awa ne yadda mata jarumai idan sun shiga al’umma sai a baibayesu ana ta nuna musu kauna amma da zarar basa wajen kuma sai labarin ya sha banbam.