Yawaita Amfani Da Kafofin Yanar Gizo, Na Haifar Da Bakin Ciki!

Kafofin Sadarwar Zamani

An gabatar da sakamakon bincike da ya tabbatar da cewar, yawaita amfani da kafofin zumunta na zamani “Social Media” na haifar da bakin ciki “Damuwa” mujallar Hallayan dan’adam wajen amfani da kwanfuta “Computer in Human Behavior” ta jami’ar Pittsburgh dake kasar Amurka.

Jerin farfesoshi, sun gano cewar, akasarin matasa da kanyi amfani da shafufuka irin su facebook, whassapp, twitter, da makanatan su a kowane lokaci, suna shiga cikin damu, bisa dalilin kosawa da su kanyi wajen ganin an karanta labarin su, ko kuma kokarin sanin makomar wasu labarai.

Duk matasa da kanyi amfani da shafufuka da suka kai bakwai 7, zuwa goma sha daya 11, suna kusa da kamuwa da cutar tashin hankali. Bisa sauran matasa da kanyi amfanida kafa daya 1, zuwa biyu 2. Duk dai da haka idan akayi la’akari da irin awowi da matasa kan kashe wajen bincike a kafofin, za’a ga cewar matsalar duk dayace.

Likitoci da dama sun bayyanar da sakamakon binciken da suka gudanar, a kan matasa masu dauke da cutar damuwa, ko rashin annuri, da ya bayyanar da cewar, mafi akasarin matasan suna amfani da kafofin sadarwa da yawa, wanda hakan shi ke haifar musu da cutar dake damun su.

Binciken dai ya cigaba da bayyanar da wasu abubuwa da kan haddasa kamuwa da irin wadannan cututtukan, da suka hada da yadda mutane kan karanta wasu abubuwa, wanda zasu iya bata musu rai cikin kankanin lokaci, wanda maganin wannan damuwar takan iya daukar lokaci kamun ta gushe.

Don haka akwai bukatar matasa da ma’abota amfani da wadannan kafofin, na zumunta da su rage amfani da kafofin, musamman idan dare yayi. Kuma a kokarta samo wasu hanyoyin sada zumunci, ba dole sai ta hanyar yanar gizo ba.