WASHINGTON, DC —
Suma ba’a bar su a baya ba, shafin zumunta na Twitter, sun kaddamar da damar bidiyo kai tsaye. A wani rahoto da suka fitar a shafin kamfanin cewar, suma yanzu baza su bari a ce kamfanin Facebook ne kawai yake bada wannan damar ba.
Abu kawai da mutun yake bukata shine ya shiga shafin shi, sai yaje inda aka sa “Live” don fara amfani da bidiyon shi kaitsaye. Duk wanda ke kallon bidiyon da mutun yake dauka a yayin da yake daukan, zasu iya magana da shi ta sakon rubutu, suma kaitsaye.
Hakan zai ba mutane damar bayyanar da kansu cikin sauki, da nuna halin da suke ciki idan suna da bukatar hakan. A nan ba da jimawa ba mutane masu wayoyin Android, da iOS, zasu fara more wannan garabasar.