Solomon Timothy Anjide, matashi ne dan asalin jihar Nasarawa. An haife shi a garin Jos, inda ya yi makarantar firamari. Da ga nan yayi karatun sakandire a kwalejin Barewa dake Zaria. A shekarar 2010, Solomon ya kamala karatun digiri a kimiyyar siyasa a jami'ar Nasarawa, dake Keffi. A shekara 2011, Solomon ya yi bautar kasa a makarantar mata dake Old Airport Road Minna, a Jihar Niger.
A yunkurin neman karin ilimi, Solomon ya wuce zuwa Birtaniya, inda ya kammala karatu a matakin digiri na biyu, a shekarar 2014, a jami’ar “Swansea” da ke Wales, duk a kasar Ingila. Da ga nan ya samu aikin koyarwa a sashen kimiyar Siyasa ta “Federal University” Lafia, jami’ar tarayya dake Lafia.
Babban burin Solomon, ya samu ilimi mai zurfi, hakan yasa ya koma kasar Birtaniya, don karatun digirin digirgir “Ph.D” a bangaren tsaro da zaman lafiya. Solomon yana koyar da dalibai a jami’ar Lincoln, a yayin da yake karatun digiri na uku. Zuwa yanzu ya gabatar da kasidu a taron karama juna sani da nemo hanyoyin magance ta’addanci, na rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram, da dama a kasar Ingila, haka da Jamhuriyar Ireland da kuma Najeriya.
Solomon, matashi ne mai kishin ganin cewa, matasa ‘yan uwan shi a Najeriya, a ko’ina su samu cigaba da ya kamata. Yana da tabbacin cewa matasa sune manyan gobe, don haka duk wani cigaba da wata kasa ta samu a yanzu yana da nasaba da gudunmawar matasa.