Taron masana binciken arzikin karkashin kasa da abubuwan tarihi, sun hako kasusuwan wata hallita mai kama da mutun, a wani daji dake kasar Tanzania, kasusuwan basu kama da na mutanen wannan zamanin. Domin kuwa tsawon jikin kasusuwan sun kai zira’I goma sha uku 13.
Tsayi da girman kwakwalwar kwarangwal din, tana kamada na samudawa, binciken su ya bayyanar musu da cewar, wadannan kasusuwan sun kwashe tsawon shekaru sama da milliyan uku da dubu dari bakwai 3.7M.
Wannan shine kwarangwal mafi tsawo da suka taba zakulowa, ko suka taba gani a wannan duniyar. Tun dai a shekarar 1970, antaba samun wani kwarangwal a yankin Laetoli, amma ba’a taba samun irin wannan ba.
Masannan sun lakama wannan kwarangwal din suna “S1” wanda yake da nauyi da yakai kilogram arba’in da biyar 45, kusan nauyin buhun siminti. Wannan kwarangwal din yafi girman wanda aka taba samu a kasar Habasha “Ethiopia” da mita bakwai 7. Babu wata alama da ta iya nuna cewar, halittar kwarangwal din na mace ne ko na miji.