Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook: Labaran Da Su Kayi Kaurin Suna A Shekarar 2016!


Tambarin Kamfanin Facebook
Tambarin Kamfanin Facebook

Shafin zumunta na facebook, sun bayyanar da rahoton su, da yake nuni da wasu labarai sune labaran da su kafi zama abun tattaunawa, a wannan shekarar dake neman karewa. Babban labarin da yafi samun mutane wajen aunawa, da fashin baki, shine zaben kasar Amurka, da aka gabatar a watan da ya gabata.

Tun a shekarar 2015, dai labarin zaben kasar ya fara daukar wuta, wanda a cikin wannan shekarar kuwa abun ya kai duk inda ba’a taba tsanmani ba. Labari dake bimishi kuwa shine, labarin siyasar kasar Brazil, haka na gaba kuwa shine labarin wasan bidiyo da aka kirkira a tsakiyar wannan shekarar, mai take “Pokemon Go”

A gaba kuwa shine labarin kungiyar rajin kare hakkin mutane bakake mai take “Black Lives Matter” kungiyace da take kasar Amurka, dake kokarin kwatoma bakaken mutane hakkin su a wajen turawa. A gaba kuwa sai labarin shugaban kasar philippine Mr. Rodrigo Duterte, tare da zaben shi, duk da cewar shine shugaban kasa na farko da ya fito fili, ya nuna adawar shi da nuna rashin yarda da yadda kasar Amurka, ke shiga al’amuran wasu kasashe a duniya.

Haka ma labarin wasanin Olympics, sai labari nagaba shine, labarin Firaministan kasar Birtaniya, kana labarin mawaki David Bowie, baki daya a karshe sai labarin mutuwar shahararren dan wasan danbe “Boxing” Muhammad Ali.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG