Kamfanin Sufuri Na "Uber" Sun Fara Haya Da Mota Mai...!

Motar Haya Ta Kamfanin Uber Mai Tuka Kanta

Kanfanin motocin sufuri na “Uber” sun kaddamar da mota mai tuka kanta ga jama’a. A karon farko kamfanin sun samar da wannan motar ne don mutane su dinga dauka haya. Ita dai motar batada matuki, abu kawai da mutun yake bukata shine, idan mutun ya shiga motar sai ya rubuta mata adireshin inda yake son zuwa.

Motar dai tana amfani da na’urar kwamfuta, wajen kamo siginar a na’urar tauraron dan’adam dake cikin sararrin samaniya. Daya daga cikin manya-manyan garuruwa a kasar Amurka, San Francisco, su zasu fara morema wannan sabuwar fasahar.

A tabakin mataimakin shugaban kamfanin Mr. Anthony Levandowski, motocin dai an kayatar da su, da na’urorin zamani da suke da matakan tsaro matuka, da babu wani hadari da zai iya samun mutun, ayayin tafiya cikin mototar.

Suma kamfanin Google, sun kara kaimi wajen ganin sun bayyanar da tasu motar mai tuka kanta nan bada jimawa ba. Duk abokan hurda da kamfani, zasu samu sauki idan sukayi amfani da sabon tsari na “UberX ride” kudin haya bazai kai yawan kudi idan mutun ne zai tuka motar ba.