Gwamnatin Jihar Gombe Da Hadin Gwiwar Hukumar Muradun Karni Sun Horas Da Matasa 1000

Gwamnatin jihar Gombe tare da hadin gwiwar hukumar muradun karni sun horas da matasa dubu daya game da sha’anin tsaro da kuma ayyukan kiwon lafiya.

Wadannan matasa za’a turasu makarantun firamare ne dakuma na gabada firamare domin gudanar da ayyukan da aka koya musu.

An gudanar da bikin yaye matasan ne a sansanin da suka sami horo na tsawon makonni biyu a garin wuro dole dake kan iyakar jihohin bauchi da gombe.

A cewar Malam Faruk Yarma shine kwamishinan inganta rayuwar matasan jihar Gombe, ya yi Karin haske cewar “a yunkurin samarawa da matasa aikin yi ne aka horas da wadannan matasa da aka yiwa lakabi da Education Marshals, da za’a tura domin kula da makarantu a fadain jihar”.

“za su yi aiki kafada da kafada da makarantun inda zasu rika bada ayyukan daukin gaggawa, da tsaro da kuma ayyukan tallafi na jinkai.

Domin Karin bayani, ga rahoton Abdulwahab Muhammed.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Gombe Da Hadin Gwiwar Hukumar Muradun Karni Sun Horas Da Matasa 1000