Rahma Sagir Adam, daya daga cikin 'yan makarantar Hasiya Bayero, dake jihar kano, kuma daga cikin daliban da suka shiga gasar makarantu 600, da kungiyar White Horse Risk Management ta shiryawa daliban makarantun a jihar Kno, ta kuma lashe wannan zabe.
Ta kirkiri gida, adaidaita sahu ,kayan daki da sauransu ta ce tana samun hikimar aiwatar da abubuwanne a kowanne hali ta tsinci kanta , inda ta ke zuwa ta sayi robalin wanda da shi ne take kire-kirenta .
Daga Rahma sai muka canza sheka inda muka tattauna tare da wani mai bukata ta musammam wanda shima ya shiga wannan gasar, Ibrahim Abubakar daga makarantar G.C Kwakwaci, wanda shi kuma keken guragu ya kirkira amma fa na zamani inda yayi wa keken kwaliya tare da kawata shi.
Ya ce da kansa ya hada keken kama daga yanka rodi zuwa hada shi a wajen mai welda daga nan ya hada ragowan keken.
Da ya fara hada keken guragu sai ya kai Katsina road inda ake sayar da keken guragun suka ce masa zasu ajeye ko za’a saya, a hankali har aka saye kekunan da yayi tare da bashi shawarar zasu dada koya masa yadda ake hada keken da haka ne ya kai inda yake a yanzu
Ko da yake a yanzu da kansa yake hada komai da komai da lankwasa keke zuwa karshe , kuma fatansa dai bai wuce ya zamo injiniya ba.
Your browser doesn’t support HTML5