A jihar Bauchi, jami’an tsaro sun tarwatsa wasu matasa maza da mata fiye da dubu daya wadanda suka fito daga jihohin arewa goma sha tara domin samu horo mai nasaba aikin damara.
Ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar Bauchi ne tasa jami’an tsaro sun tarwatsa matasan dake sansanin wasanni da ake kira “Games Village” dake cikin garin Bauchi, a sanadiyar gano cewa wani mai suna Usman Shuaibu Dass, ya shirya damfara ta hanyar yin amfani da takarda mai dauke da tambarin jam’iyyar APC, ya barbi kudin matasa.
Wakilin muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad, yace bincike, ya nuna cewa Usman Shuaibu Dass, shine ya shirya ne ya shirya bada horon matasan inda ya umarci matasan dasu kudade a Banki, domin samun horon da zai basu dama a daukesu aiki mai nasaba da damara.
Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, Ibrahim Madaki Saleh, ya ce an zo masu da suffan APC “Patriotic Front” dalilin da yasa suka samu ganawa amma daga baya sai hedkwatan APC, tace bata da wani alaka dasu.
Daya daga cikin matasan Muhammad Nazif Abubakar, daga jihar Jigawa cewa yayi lalle idan Gwamnati tace bata da masaniya, haka yana nuni da cewa za’a iya, tara wasu bata gari sama da dubu daya ace Gwamnati bata sani ba wannan lallai abun a duba ne.
Shi kuwa wanda ya shirya taron Usman Shuaibu Dass, cewa yayi gidan gwamnati jihar Bauchi, duk wani abu na ci gaba basu so.