Babbar kotun jihar Osun, ta yankewa wani matasi mai shekaru talatin da biyar hukumcin kisa ta hanyar hatayewa har sai ransa ya fita.
Shi dai wannan matashi, mai suna Kayode Idowu, an sameshi da laifin fashi da makami ne da kuma kisa.
Kayode Idowu, da Femi Adewale, a ranar 3, ga watan Agustan, da ya gabata suka kai farmaki gidajen wasu mutane inda basu yi nasarar samun kudi sai suka kashe wata mata mai suna Florence Ajayi.
Mai gabatar da kara na Gwamnati ya fadawa kotu cewa na biyu da ake zargi da aikata wannan aika Femi Adewale, yamutu.
Ita kuwa Lauya mai kare barayin Sade Ipede, ta roki kotu da ta nuna tausaya da sassauci.
Bayan da ta ji bayanan lauyoyin mai shara’a, Kudrat Akano, tace mai gabatar da kara bada bayanai da shedu da suka gamsar da kotu saboda haka sai ta zartar da hukuncin kisa.