Kamfanin Huawei ya kaddamar da wata manhajar waya a Najeriya wadda mutane zasu rika amfani da ita wajen kwashe bayanansu daga na’urar waya zuwa wata na’urar wayar cikin sauki. A cewar Huawei, wannan manhaja dai yanzu haka za a iya sauke ta akan wayoyi kyauta.
Wannan manhaja dai za a iya amfni da ita wajen sauke duk wasu bayanai wanda suka hada da lambobin waya da hotuna da duk wani sauti kamar wakoki da hotunan bidiyo dake cikin waya hannu zuwa wata wayar hannun.
Kamfanin Huawei yace yana duba yiwuwar kirkirar wata manhajar da zata iya amfani akan baki daya wayoyin dake amfani da manhajojin Apple da Android.
Kafin zuwan wannan sabuwar fasaha dai mutane kan yi amfani da SD card wajen daukar bayanai daga waya zuwa waya.
Wannan dai wata hanya ce mai sauki kuma mai nagarta wajen daukar bayanai daga waya zuwa waya, ba tare da baka lokaci ba.
Your browser doesn’t support HTML5