Kadan Daga Cikin Wasu Tsibirai, Da Su Kafi Hadari A Fadin Duniya!

A tsari da yanayi da ake ciki a wannan karnin na ashirin da daya 21, mutane a fadin duniya kanyi tunanin cewar, suna iya yawon shakatawa musamman zuwa wasu tsibirai a fadin duniya. A nasu iya tunanin shine, idan suna da lokaci, da kudi kuma suna iya zuwa ko ina a irin lokacin da suke da bukata.

Bincike ya tabbatar da wasu tsibirai a fadin duniya, suna da hadari mutane su ziyarce su. An bayyanar da wadannan tsibiran a matsayin tsibirai da su kafi kowane tsibiri hadari a duniya. Tsibirin “Izu Islands” dake kasar Japan, yana da matukar hadari ga rayuwar dan’adam, domin kuwa akan samu wata irin mashahuriyar wuta, da take addabar mutane, domin ko a shekarar 2000 sai da aka tada mutane a tsibirin.

Tsibirin “Saba” dake kasar Nertherlands, shima yana da matukar hadari, a yanki akan samu matsannanciyar iska, da take kwashe komai, tsibirin dai yafi dadin zuwa a lokacin hunturu. Tsibirin “Gruinard Island” dake yankin Scotlan a kasar ingila, yana daga cikin tsibiri da ke da hadari ga lafiyar dan’adam, domin kuwa an taba samun wata annoba da ta yada wata cuta mai kisa.