Kakakin rundunar soji mai kula da 13 Brigade, dake Calabar, ta jihar Cross River Capt Kayode Owolabi ya bayyana cewa jami’in sojannan Musa Lawal wanda ya yi ikirarin cewar an sace da kuma yin garkuwa da shi a Calabar, ranar alhamis data gabata ba gaskiya cikin lamarin.
Lawal, wanda ke aiki a karkashin rundunar sojin jihar 13th Brigade, ya ce ‘yan bindigar sun sace shi ne jim kadan bayan ya fito daga banki akan babbar hanyar data ratsa cikin Calabar, babban birnin jihar.
An baiyana cewar ‘yan bindigar sun sace sojannne da misalign karfe goma na safe, inda suka saka shi cikin mota kana suka arce da shi zuwa wani wurin da ba’a sani ba.
Mujallar Daily Post ta baiyana cewa rahotanni da dumi duminsu sun baiyana cewar Lawal da kansa ya shirya satar da ya ce anyi masa domin ya sami damar zuwa wuraren da yake bukata ba tare da sanin kowa ba.
Kakakin ya kara da cewa babu wata maganar sace shi da aka yi, domin ta yaya za’a sace mutum tsakiyar garin Calabar ba tare da daukar hankalin jama’a ba, la’akari da yadda ya ce an kama shi tare da turashi cikin mota da karfi, musamman ma soja sanye da kakinsa.
Rahotanni sun bayyana cewar bincike ya gano cewar Musa Lawal ya yi balaguro ne zuwa gidan wata budurwarsa dake Port Harcourt a jihar Rivers