Kowane Dan Wasan Kungiyar Kwallon Kafa Ta U23, Ya Sami Kudi Dala $14000

Kowane dan wasa cikin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya masu kasa da shekaru 23, da haihuwa sun ya sami zunzurutun kudi dalar Amurka dubu goma sha hudu, $14,000 kawatankwacin Naira miliyan hudu kenan daga cikin kudin da attajirin likita dan kasar Japan, Katsuya Takasu, ya basu kyauta a lokacin da suka taka leda a wasannin motsa jiki na Rio Olympic.

Kungiyar ‘yan wasan ta lashe kyautar tagulla a wasannin motsa jiki na Rio inda attajirin likitan dan kasar Japan ya basu kyautar kudi dalar Amurka dubu dari uku da tasa’in da tara $390,000, sakamakon ra’ayin ‘yan wasan da ya shigar masa rai.

Bayan watanni uku da al’kawarin da likitan yayi masu, kowane dan wasa ya sami nasa kudin kamar yadda ya al’kawarta masu.

Koda shike ‘yan wasa goma sha takwas wadanda suka taka leda a wasan karshe ne suka sami $14000, sauran wato, Taiwo Awoniyi, da Stanley Dimgba, da Yusuf Muhammed, da kuma Godwin Saviour, wadanda suka zauna a benci lokacin wasan sun sami Naira miliyan guda guda.

Ana kyautata zaton cewa babban kocin kungiyar Samson Siasia, ya sami kaso mafi tsoka daga cikin kudin.