‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles zasu sanya sababbin kayan wasa, a lokacin da zasu fafata wasa tsakaninsu da kungiyar kwallon kafa ta Algeria a wasannin shiga gasar cin kofin duniya da za a buga a shekarar 2018, cikin karshen wannan makon.
A shekakarar 2015, hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF ta rattaba hannu da kamfanin NIKE har ta tsawon shekaru uku da watanni shidda, inda kamfanin zai samarwa da ‘yan wasan kayan wasa da kudinsu suka kai kwatankwacin dala miliyan uku da dubu saba’in da biyar.
Sababbin Kayan wasan da zasu sa a gida nada launin Kore, da kuma ratsin fari a daga baya a kusa da kwalar rigar, yayinda wadanda zasu sa idan sun fita waje kuma farar riga ce mai ratsin kore a gefe gefen rigar da kuma gageren wandon.
Daman Alex Iwobi me bugawa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ya taba sa kayan tunda dama dan wasa ne dake yi wa kamfanin NIKE talla.
Ya rubuta a shafinsa na tweeter inda ya ce “ na ganawa in ganmu muna taka leda cikin sabbin kaya a karawarmu da Algeria ranar Asabar.
‘yan kungiyar kwallon kafa U-23, suka fara sa sababbin kayan kwallo na kamfanin NIKE, a wasannin motsa jiki na Rio Olympics da aka yi a shekarar 2016, inda suka lashe lambar Tagulla.