Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Zaben Amurka: Donald Trump Ya Lashe Zaben Kasar Amurka


Zabbaben Shugaban Kasar Amurka Donald J. Trump
Zabbaben Shugaban Kasar Amurka Donald J. Trump

Yadda ake gabatar da zaben shugaban kasa a kasar Amurka, yana da banbanci da yadda ake gudanar da zabe, kusan a ko'ina a fadin duniya. Mafi akasarin kasashen da ake mulki irin na demokaradiyya, za’a ga cewar wajen zabe akanyi amfani da dan takara da yafi yawan kuri’u da aka jefa a matsayin zababben shugaban kasa.

Amma a kasar Amurka abun yana da banbanci, domin kuwa akwai wasu zababbun mutane da kanyi zaben shugaban kasa, ko bayan al’umar kasan sun jefa kuri’ar su. Wanda idan dan takara ya samu rinjaye, a kuri’un daga wadannan mutanen dari biyar da talatin da takwas 538, sune zabbabun mutane da suke zaben shugaban kasa a madadin al’umar kasar Amurka.

Idan dan takara ya samu rinjayen wadannan zababbun mutanen, da ya kai dari biyu da saba’in 270, to shike nan mutun ya zama zabbaben shugaban kasar Amurka. Sakamakon zaben da aka fitar wanda aka gwambza tsakanin Hillary Clinton, ‘yar takarar jam’iyar “Democrat” da hamshakin mai kudin Donalt Trump na jam’iyar “Republican.”

Dan takarar jam’iyar Republican Donald J. Trump, shi ne wanda ya lashe zaben kasar Amurka. Yanzu ya zama zabben shugaban kasar Amurka. Za’a rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu na shekarar 2017. idan Allah ya kaimu, wannan babban abun tarihi ne a siyasar demokaradiyya a fadin duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG