A jiya ne Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal kuma zakaran kwallon kafa na nahiyar turai mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya lashe lambar yabo ta gwarzon dan wasa a bangaren La-liga na kasar Spain wato (Marca's Best player award of La-liga 2015/2016).
An kiyasta cewa Ronaldo ya zurara kwallaye har guda talatin da bakwai, ya kuma taimaka an jefa kwallaye guda goma sha daya a gasar La-liga da ta gabata a shekarar 2015/2016.
Cristiano Ronaldo, ya bayyana jin dadinsa bisa wannan lambar yabo da ya samu, ya kuma ce yau wata rana ce a gareshi mai muhimmanci wadda yake cike da farin ciki.
Cristiano, ya kara dacewar wannan abin zai sa ya kara kwazo a gasar wasan La-liga, ta bana dama sauran wasannin kwallon kafa a duniya.
A kwanakin baya ne Ronaldo, ya ayyana cewar yana da karfin guiwar ci gaba da wasa har nan da shekaru goma masu zuwa, a yanzu haka dai Ronaldo, yana da shekaru talatin da daya da haihuwa.
A litinin da ta gabata ne dai dan wasan ya kara rattaba hanu a Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, har na tsawon shekaru uku masu zuwa inda kwantirakinsa ta farko zata kare a shekara ta 2018, amma a yanzu sai shekara ta 2021, kuma ana sa tsammanin zai rika karbar kudi fam dubu £500,000, a kowane sati a kungiyar ta Real Madrid.