Jerin Kasashe Da Su Kafi Zaman Lafiya A Fadin Duniya!

La plataforma&nbsp;cultural independiente&nbsp;<em>Caracas Arte Actual</em>&nbsp;le contó a la <strong><em>Voz de América</em></strong> que la idea nació con la llegada de varios de los directivos de la plataforma a Colombia.&nbsp;

Bincike da wata hukuma mai zaman kanta ta gabatar “Global Peace Index” rahoton ya duba kasashe dari da sittin da uku 163, da amfani da wasu alkalumma ashirin da uku 23, wajen gano kasashen da su kafi zaman lafiya a fadin duniya.

Ganin cewar yanzu zaman lafiya yayi wuya, a tsakanin al’umma da kasashe. Wannan rahoton ya bayyanar da wasu kasashe a fadin duniya, da su kafi samun zaman lafiya, a rahoton da aka fitar na shekarar 2016. Kasar Iceland, itace kasa ta farko da zaman lafiya yake ruwan dare.

Kana kasar Denmark, na biye sai kasar Austria, daga nan sai kasar New Zealand, haka kasar Portugal, na biye. Itama kasar Czech Republic, ta shiga sahu, sai kasar Switzerland, da kasar Canada, kana kasar Japan, da kasar Slovenia, sai kasar Finland, haka kasar Ireland, na biye su kuwa kasar Bhutan da kasar Sweden, da Australia ba’a bar su a baya ba.