Kamfanin Apple ya bayyanar da irin ribar da suka samu, da takai kimanin damar Amurka billiyan tara $9B, a karshen shekarar bana. Kamfanin dai sun ruwaito yawan kudin da suka samu, a siyar da wayar iPhone da su kayi, kimanin dallar Amurka milliyan arba’in da biyar $45M.
Duk dai da cewar sun fuskanci karanci kasuwa a shekarar bana, domin kuwa a shekarar da ta gabata sun samu kudi a cinikin wayar iPhone, da ya kai dalar Amurka milliyan arba’in da takwas $48M. Yanzu haka dai kamfanin na cigaba da fuskantar wasu ‘yan matsaloli da ke da alaka da irin yadda suke gudanar da kasuwancin su.
Masana dai na ganin cewar, babbar matsalar kamfanin Apple itace kamfanin na bukatar kwararrun masana harkar kasuwanci, da sanin abubuwa da mutane ke bukata, a takaice kamfanin sune matsalar kamfanin. Ana ganin idan kamfanin basu fito da wasu sabbabin hanyoyi da suka kamata ba, zasu iya rasa kasuwar su a nan gaba kadan.