WASHINGTON D.C —
Na dauki waka tamkar sana’a kuma burina a harkar waka dai shine na fadakar , ta hanyar inganta rayuwar al'umma tare da fatan al'umma su karbi sakonninsa , inji mawaki Jamilu.
Jamilu Y Adam , wanda aka fi sani da Jamilu Hagi,ya fara waka ne tun makarantar islamiyya a lokacin maulidi mafi yawan lokuta shi yake rerawa
Bayan makarantar ma ya lura mutane na nishadantuwa ta hanyar sauraron waka, kuma ya fara ne shekaru goma sha takwas da suka wuce.
A fanninmu na tsegumi kuwa duban masoyan daya daga cikin mawakan nan na Psqaure wato Peter ne suka yi tir da wata shiga da yayi wadda a cewar su bata dace da shi ba kuma ta saba da al’audunsu da dabi’un kasarsu.
Masoyan nasa sun ce abinda yayi bai dace ba domin kuwa yana da mata da ‘yaya.