Matasa Na Amfani Da Kimiyyar Zamani Wajen Satar Ansa!

Hanyoyin Sadarwa na Zamani.

Satar ansa a jarabawa ba bakon al’amari bane, abunda ya zama bakon al’amarin shine, yadda dalibai suka gano wata sabuwar hanya ta satar ansa yanzu. Kamar yadda aka sani dalibai na rubuta satar ansa a hannu, yanzu ba a hannu ake rubuta wa ba.

Sabuwar hanyar kimiyya ta sa matasa kirkiro wata sabuwar hanyar satar ansa, da take basu damar yin satar ansar jarabawar a saukake. Masanin kimiyya kuma kwararre a fagen dandalin sadarwa na zamani Mr. Nile Nickel, yace dalilin da yasa yanzu dalibai ke amfani da sabbabin na’urorin sadarwa, wajen satar ansar jarabawa shine, saboda yawan da su kayi a ako ina.

Idan aka duba sakamakon binciken hukuma “Pew” data fitar ‘yan kwanakin nan dake nuni da cewar, yanzu yawanci kowa yana da waya wanda ya kai kashi talatin da uku a cikin shekarar dubu biyu da sha daya.

Sabo da haka yanzu kowa ya mallaki wayar sadarwa, kuma yana amfani da ita, idan dai ba za’a kama niba, kuma kowa nayi ai shikenan. Ka dauki wayar sadarwa ko na’urar lissafi kalkuleta.

Akwai abubuwa da yawa da za’a iya boyewa a cikin su, yace akwai wasu gilasai na ido da na yanar gizo, da suke iya daukar hotuna da adana su, a wani karamin muhallahi wanda ya hada da agogon hannu, ta yadda idan sun kalla zasu rubuta satar ansar su.