Tun ba yau ba, kamfanin Goole suka fara kera wayoyin su ba, tare da hadin gwiwar kamfanin Nexus, jiya ne kamfanin suka bayyanar da cewar, zasu fara kirkirar tasu sabuwar wayar da kashin kansu, wadda suka sama suna “Pixel da Pixel XL”
Wadannan wayoyin zasu zama na farko da za sazo dauke da duk wasu abubuwa da kamfanin na Google, ke kerawa batare da mutun ya bukaci kara saukar da manhajojin ba. Wadannan wayoyin suna dauke da wasu abubuwa da babu wata wayar zamani da take dauke dasu.
Wayoyin zasu zo dauke da wata dama da mutun zai samu mazubin ajiya, a yanar gizo da bashi da adadi. Sun inganta kyamarar wayar da wasu damanmaki da wayar suke dauke da su, da su kafi na duk wata wayar zamani.
Wayoyin yanzu haka suna kasuwa, akan farashin dallar Amurka, $649 dai-dai da naira dubu dari biyu da talatin, tana da girman gilashi, da sauri da yakai kimanin gudun jirgi a sararrin samaniya.