WASHINGTON, DC —
Masana na cigaba da zurfafa bincike, wajen maida
mutun-mutumi “Robot” tamkar mutun, shahararren kanfanin
kera robot na kasar China, sun kirkiri wani sabon mutun-mutumi,
da suka sama suna “Nxrob”, da yake mu’amala da mutane kamar
yadda mutane suke gabatar da zaman takewar su, a tsakanin
jinsin dan’adam.
Shi dai sabon mutun-mutumin yakan gabatar da duk wasu
abubuwa, da mutun kanyi a gida, kamar su kunna talabijin,
kunna na’urar na'urar dimama daki, da sanin irin yanayin da
ya kamata mutun ya zauna a cikin daki, yana fira da mutun don
bashi labarin dari, da abun ban mamaki.
Haka mutun mutumin, yakan yi wasa da yara, da tuna musu
wasu abubuwa da ya kamata ace sunyi, a kowane lokaci a rana,
yakan tunama yaro cewar an bashi aikin gida daga makaranta,
don haka sai ya kokarta wajenyi.
Bai tsaya nan kawai ba, yakan san kowane mutun da yake a
cikin gida, da irin abun da kowane mahaluki yake bukata,
kamar irin kalan kayan da mutun yake so, da irin abincin da
mutun yafi so.
Haka idan dakin mutun yayi sanyi ko zafi, bayan
mutun na bacci, roboto din yakan sauya yanayin dakin wajen
kunna na’urar da zata maida dakin wajen zama, batare da
damuwa ga lafiya mutun ba.